Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data
Majalisar ta ce har yanzu babu tsayayyen layin waya mai sabis mai kyau a cikinsu.
![Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/05/House-of-Reps-1.jpg)
Majalisar Wakilai ta buƙaci Hukumar Kula da Sadarwa (NCC) ta janye ƙarin kashi 50 na kuɗin waya da data da ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ɗan majalisar daga Jihar Bayelsa, Oboku Oforji ya gabatar da ƙudirin kan lamarin.
Majalisar ta ce ƙarin bai kamata ba a wannan lokacin, saboda har yanzu babu tsayayyen layin waya mai sabis mai kyau a cikinsu.
- Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya
- Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su
A don haka ne majalisar ta buƙaci NCC da Ministan Sadarwa, Bosun Tijani, su dakatar da ƙarin saboda matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fama da shi.
Alƙaluma dai na nuna daga watan Disambar 2023 zuwa yanzu, jimillar ‘yan Najeriya miliyan 224 ne ke amfani da layukan waya.
Alƙaluman sun kuma nuna MTN ne ka kan gaba da kashi 38.79 da adadin kwastamomi miliyan 87, sai Glo da Airtel masu miliyan 61, sai 9mobile mai miliyan 13.9.
Daga cikin kamfanonin kuma, MTN tuni ya fara ɗabbaka ƙarin kashi 50 akan kuɗin data da kiran waya.