Majalisa ta amince a tsawaita wa’adin aiwatar da Kasafin Kuɗin 2023

An tafka zazzafar muhawara gabanin amincewa da ƙudirin da Shugaba Tinubu ya miƙa wa majalisar.

Majalisa ta amince a tsawaita wa’adin aiwatar da Kasafin Kuɗin 2023

Zauren Majalisar Wakilai

Majalisar Wakilai ta amince da buƙatar ci gaba da aiwatar da Kasafin Kuɗin 2023 har zuwa ƙarshen shekarar 2024.

Hakan dai na kunshe ne cikin ata sanarwa da majalisar ta fitar ta hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Akin Rotimi.

Ya bayyana cewa, “an amince da ƙudurin ne domin amfanin ƙasa baki ɗaya, bayan zazzafar muhawara da aka tafka kan lamarin.”

Sanarwar ta ce “Majalisar wakilai ta amince da dokoki biyu waɗanda suka buƙaci tsawaita aiwatar da kasafin kuɗi na 2023 da kuma ƙaramin kasafin kuɗi na shekarar ta 2023 har zuwa watan Disamban 2024.”

Ana iya tuna cewa dai Shugaba Bola Tinubu ne ya tura ƙudurorin biyu zuwa majalisar dokoki.

A lokacin muhawara kan ƙudurorin, wasu ’an majalisa sun nuna shakku game da buƙatar amincewa da su cikin sauri, inda suka yi fargabar kada ya kasance akwai wani abu da zai cuci al’ummar ƙasa.

Daga cikin waɗanda a farko suka yi tirjiya kan aiwatar da ƙudirin har da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda da tsohon bulaliyar majalisar, Alhassan Ado Doguwa.

Sai dai bayan tattaunawa da kuma duba ɓangarorin dokar a matakin kwamiti, zauren majalisar ya sake zama inda ya amince da ƙudurorin.