Majalisa ta amince da Amaechi
Majalisar Dattawa da ke aikin tantance ministocin Gwamnatin Shugaba Buhari, ta Amince da tsohon Gwmanan Jihar Ribas Rotimi Amaechi, bayan da ya sha gwagwarmya, inda aka yi ta dage ranakun tantance shi. Wannan al’amari na Cif Rotimi Amaechi ya dauki hankalin al’ummar kasar nan, har ta kai ga kowa na jiran ranar da za a […]
Majalisar Dattawa da ke aikin tantance ministocin Gwamnatin Shugaba Buhari, ta Amince da tsohon Gwmanan Jihar Ribas Rotimi Amaechi, bayan da ya sha gwagwarmya, inda aka yi ta dage ranakun tantance shi. Wannan al’amari na Cif Rotimi Amaechi ya dauki hankalin al’ummar kasar nan, har ta kai ga kowa na jiran ranar da za a tantance shi.
Mista Amaechi, wanda ya kasance Daraktan-Janar na yakin neman zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya samu amincewar majalisar ne bayan da aka sha takaddama da dage ranakun tantance shi, al’amarin da aka ta’allaka da korafin da wasu ’yan adawa suka gabatar wa majalisar a kansa.
An sha mamakin jin cewa, dan Majalisar Dattawa, tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom. Godswil Akpabio ya sanar da cewa gungun ’yan jam’iyyar PDP ba su da tambayoyin da za su yi wa Rotimi Amaechi, don haka shugaban masu rinjaye a majalisar, Ali Ndume ya bukaci Amaechi da ya yi wa majalisar gaisuwar bangirma ya fice. Amma sai aka samu takkadamar rashin yardar ’yan majalisar a kan wannan matsaya da ya yanke, inda wadansu suka ce za su yi masa tambayoyi, ba tare da la’akari da ra’ayin rukunin ’yan jam’iyyar PDP ba.
Duk da haka shugaban majalisar, Bukola Saraki ya ba shi irin kulawa ta musamman da suka saba bai wa tsofaffin ’yan majalisa, amma ’yan majalisar suka jajirce kan cewa lallai sai sun yi masa tambayoyi.
Tsohon Gwmanan ya samu amincewa ne, bayan da ya sha tambayoyi daga ’yan majalisar, wadanda wadansunsu sun yi aiki tare da shi a lokacin da yake Gwamna a Jihar Ribas.