Majalisa ta amince da amfani da na’urar ‘Card Reader’ a zaben 2019
Majalisar dattawan Najeriya ta sake duba batun amincewa da gyaran fuska ga dokar zaben Najeriya, inda a yanzu majalisar ta amince da amfani da na’urar ‘Card Reader’ don tantance masu kada kuri’a. A zaman majalisar dai an sha takaddama tsakanin bangaren majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa game da dokar amfani da na’urar. Batun […]
Majalisar dattawan Najeriya ta sake duba batun amincewa da gyaran fuska ga dokar zaben Najeriya, inda a yanzu majalisar ta amince da amfani da na’urar ‘Card Reader’ don tantance masu kada kuri’a.
A zaman majalisar dai an sha takaddama tsakanin bangaren majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa game da dokar amfani da na’urar.
Batun amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a na daga cikin gyaran da ‘yan majalisar suka yi a tattaunawarsu.