Majalisa ta amince da duk ministocin Buhari
Bayan an shafe makonni uku ana tantance ministoci a majalisar dattawa, majalisar ta kammala tantance ministoci 36, inda a jiya Alhamis aka yi dambawar amincewa da Amaechi, tare da wasu mutum 17 a matsayin ministoci. Tun kafin a kira Mista Rotimi Amaechi gaban majalisar don tantance shi, an yi ta jan kafa, al’amarin da daga […]
Bayan an shafe makonni uku ana tantance ministoci a majalisar dattawa, majalisar ta kammala tantance ministoci 36, inda a jiya Alhamis aka yi dambawar amincewa da Amaechi, tare da wasu mutum 17 a matsayin ministoci. Tun kafin a kira Mista Rotimi Amaechi gaban majalisar don tantance shi, an yi ta jan kafa, al’amarin da daga bisani ta tabbata cewa, dambarwar siyasa ce ake ta yi, tsakanin jam’iyyarsa ta APC da kuma PDP, wadda ta zama jam’iyyar adawa. ’Yan adawa dai sun doge kan cewa lallai sai a yi watsi da maganar Amaechi bisa la’akari da korafin da aka gabatar a kansa da kuma karar da ya kai gaban kotu kan ta yi watsi da korafe-korafen da aka yi masa.
Kafin dai a tantance ministocin, an fara da amincewa da nadin Shugaban Hukumar Zabe (INEC) ne, wato Farfesa Mahmoud Yakubu da nadin kwamishinonin zabe mutum biyar Afro da Simbini da Zakari da Lecky da Soyebi.
Majalisar ta bukaci a kara wa’adin zamanta na ranar Alhamis, har zuwa bayan karfe biyun rana. Farfesa Mahmoud Yakubu ne kawai ya sha tambayoyi, inda daga bisani aka umarce shi da ya yi gaisuwa ya tafi a binsa.
’Yan majalisar sun yi ta kai ruwa rana wajen amincewa da Rotimi Amaechi, tsohon Gwamnan Jihar Ribas. Majalisar ta fara da amincewa da mutanen da suka hada da Aisha Mohammed da Adamu Adamu da Mohammed Musa Bello da Anwuka Anthony Gozie da Okechukwu Enelamah da Okechukwu Enelamah da Pastor Usani Usani da Dan Ali da Zainab Ahmed da Geoffrey Onyeama da Bawa Bwari da Adewole Folorunso da James Ocholi da Baba Shehuri Mustapha/
danmajalisa Olujimi ya ce akwai bukatar a kyale kotu ta warware matsalar Amaechi. Shi kuwa danmajalisa Sam Anyanwu, cewa ya yi, bisa la’akari da rahoton Kwamitin Tarbiyya da ka’idoji, majalisar ba ta da ’yancin tabbatar da ministan. Kuma danmajalisa Omoworare, cewa ya yi kwamitin tarbiyya da bin ka’idoji shi ne mafi muhimmanci a majalisar. Sai ya karanto kundin dokokin majalisar, inda ya yi nuni da cewa, matsalar na gaban kotu, don haka majalisar ba za ta iya yanke hukunci a kan al’amarin ba.
An yi ta ce ce – ku ce har ta kai ga ’ya’yan jam’iyyar PDP da ke majalisar suka fice, sai aka tabbatar da Rotimi Amaechi ba tare da su ba.