Majalisa ta amince da kara tiriliyan N6.2 a kasafin 2024
Malisar Dattawa ta amince da kudurin karin mafi karancin albashi zuwa N70,000. za a samo karin kudaden da ake butata ne daga harajin kazamar riba da bankuna suka samu daga canjin kudaden kasashen waje a shekarar 2023
Malisar Dattawa ta amince da kudurin kara Naira tiriliyan 6.2 a kasasfin shekarar 2024.
Hakan na mufin majalisar ta amince da dokar biyan karin mafi karancin albashi na N70,000 da shugaban kasa ya tura mata.
Majalisar ta amince da kudurin karin kudi a kasafin ne bayan sauraron jawabin shugaban kwamitin kasafin kudi, Sanata Solomon Olamilekan.
Sanata Olamilekan ya bayyana cewa daga cikin tiriliyan N6.2 din za a kashe N3.2trn a kan manyan ayyuka, ragowar N3 trn kuma a kan ayyukan yau da kullum.
- An yi wa mutum 3 ɗaurin rai da rai kan yi wa kurma fyaɗe
- Matashi ya shiga hannu kan lalata taransifoma a Adamawa
Dan majalisar ya bayyana cewa dokar karin kasafin za ta samar da karin kudaden gudanar a manyan ayyuka domin shan romon dimokuradiyya a fadin kasar da kuma biyan sabon albashi.
A cewarsa, sai da kwamitin ya gana da muhimman masu ruwa da tsaki da dama musamman ministan kasafi kan hanyoyin da za a samu kudaden gudanar da ayyukan.
Dan majalisar ya ce za a samo karin kudaden da ake butata ne daga harajin kazamar riba da bankuna suka samu daga canjin kudaden kasashen waje a shekarar 2023.