Majalisa ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin Tinubu na tiriliyan 2.17
A ranar Alhamis majalisun suka amince da kasafin
Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar Alhamis ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin 2023 da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aike mata na Naira tiriliyan 2.176.
Majalisar Dattawa da takwararta ta Wakilai dai sun amince da bukatar ce kwana biyu bayan an gabatar musu da ita a zaurukansu.
- ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 20 a wajen jana’iza a Yobe
- Gaza: Isra’ila ta kashe mutum 195 a sansanin gudun hijira
A majalisar Dattijai dai, an amince da kasafin ne bayan karbar rahoton Kwamitinta na Kasafin Kudi da ke karkashin jagorancin Sanata Adeola Olamilekan.
A ranar Talata ce dai shugaba Tinubu, a cikin wata wasika ya bukaci majalisun da su amince da hakan, a karo na biyu bayan ya aike da iri bukaci a sahale masa kashe Naira biliyan 819.5 domin rage radadin cire tallafin mai.
“Muna bukatar ku amince da wannan kasafin ne saboda mu samu damar aiwatar da wasu manyan ayyukan raya kasa, musamman hanyoyi, wadanda ya zama wajibi a fara su kafin a shiga rani, daga yanzu zuwa karshen shekara,” in ji Tinubu a cikin wasikar.
Daga cikin kudin dai, za a kashe Naira tiriliyan 1.010 ne domin ayyukan yau da kullum, yayin da za a kashe tiriliyan 1.165 domin manyan ayyuka.
A Majalisar Wakilai kuwa, an amince da kasafin ne bayan shi ma shugaban kwamitin kasafi na majalisar, Abubakar Kabir (Kano, APC) ya gabatar mata da rahoto.
Kakakin majalisar, Abbas Tajuddeen, wanda shi ne ya jagoranci zaman dai shi ne ya amince da kasafin bayan ya karanto shi sadara-sadara bayan amincewa da rahoton.