Majalisa ta amince da mutanen da shugaban kasa ya zaba

Majalisar Dattijai ta dora wa kwamitinta mai lura da harkokin bankuna da kudi alhakin fara gudanar da matakin da zai kai ga amincewa da mutum hudu da shugaban kasa ya zaba membobin kwamitin tsare-tsaren kudi na babban bankin Najeriya.   Hakan ya zo ne daidai lokacin da majalisar ta amince da wasikar da shugaban ya […]

Majalisa ta amince da mutanen da shugaban kasa ya zaba

Majalisar Dattijai ta dora wa kwamitinta mai lura da harkokin bankuna da kudi alhakin fara gudanar da matakin da zai kai ga amincewa da mutum hudu da shugaban kasa ya zaba membobin kwamitin tsare-tsaren kudi na babban bankin Najeriya.
 
Hakan ya zo ne daidai lokacin da majalisar ta amince da wasikar da shugaban ya mika mata na neman ta amince da nadin mutum hudun.
 
Wadanda aka nadan sun hada da Farfesa Adeola Adenikinju da Dokta Aliyu Sanusi da Dokta Robert Asogwa da kuma Dokta Asheikh Maidugu.