Majalisa ta amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
Majalisar ta amince da ƙudirin ne a zamanta na ranar Talata.
Majalisar Dokokin Najeriya, ta amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Wannan na cikin buƙatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisar.
- EFCC ta gaza gabatar da hujja a kan Kwankwaso a kotu
- Tinubu ya mika kudurin karin albashi zuwa N70,000 ga Majalisa
Shugaba Tinubu ya aike da ƙudurin dokar mafi karancin albashi ga Majalisar Dokoki ta Kasa don sahalewa.
Ya buƙaci majalisar datttawa da majalisar wakilai su yi la’akari da dokar cikin gaggawa.
Dokar ta nemi yin gyara a Dokar Karancin Albashi ta 2019, ta hanyar ƙara albashin daga Naira 30,000 zuwa Naira 70,000.
Shugaban ƙasa kuma buƙaci rage lokacin duba albashi daga shekara biyar zuwa shekara uku.
Aminiya ta ruwaito cewar majalisar ta duba dokar cikin hanzari da kuma amincewa da ita bayan tsallake karatu a zauren majalisar.
Idan ba a manta ba, an kai ruwa rana da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC kan batun ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Najeriya.
Amma sai a makon da ya gabata ne ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayya suka cimma matsaya a kan Naira 70,000 a matsayin sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.