Majalisa ta amince da naɗin Oluyede a matsayin Hafsan Sojin Ƙasa
Majalisar Dattawa, ta amince da naɗin Laftana Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa.
Majalisar Dattawa, ta amince da naɗin Laftana Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa.
Wannan na zuwa ne biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar mai kula da harkokin rundunar sojin ƙasa, wanda Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua ke jagoranta.
Majalisar ta ce naɗin Oluyede ya yi daidai da sashe na 217 da ƙaramin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Majalisar ta amince da murya ɗaya shawarwarin da kwamitin ya bayar a rahoton.
Shugaba Tinubu ne ya naɗa Laftana Janar Oluyede, a matsayin mai riƙon muƙamin shugaban rundunar sojin ƙasa sakamakon rasuwar, Laftana Janar Taoreed Abiodun Lagbaja.
Bayan haka, ta tabbatar da Oluyede a matsayin wanda zai maye gurbin Lagbaja.