Majalisa ta amince da nadin Emefiele da Bulkachuwa

Majalisar Dattawa ta amince da nadin Mista Godwin Emefiele a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, yayin da ta amince da nadin Mai shari’a Zainab Bulkachuwa a matsayin Shugabar Kotun daukaka kara ta Tarayya.Mista Emefiele wanda shi ne Manajan Daraktan Bankin Zenith zai soma aiki ne a watan Yuni mai zuwa, lokacin da wa’adin shugabancin […]

Majalisa ta amince da nadin Emefiele da Bulkachuwa
Majalisa ta amince da nadin Emefiele da Bulkachuwa

Majalisar Dattawa ta amince da nadin Mista Godwin Emefiele a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, yayin da ta amince da nadin Mai shari’a Zainab Bulkachuwa a matsayin Shugabar Kotun daukaka kara ta Tarayya.
Mista Emefiele wanda shi ne Manajan Daraktan Bankin Zenith zai soma aiki ne a watan Yuni mai zuwa, lokacin da wa’adin shugabancin Malam Sanusi Lamido Sanusi wanda aka dakatar zai kare.
Ita kuma Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa wacce a hanzu haka take rikon kujerar shugabancin kotun ta fito ne daga Jihar Gombe.
Shugaba Goodluck Jonathan ne ya mika sunayensu ga majalisar don ta amince kafin ya rantsar da su kamar yadda dokar kasa ta tanada.