Majalisa ta amince wa Ganduje ya ciwo bashin Naira Biliyan 20
Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da bukatar da gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar mata na neman ciwo bashin Naira biliyan 20 domin aiwatar da wasu ayyuka a jihar. Shugaban kwamitin kudi na majalisar, Alhaji Abubakar Zakari wanda ya gabatar da rahoton kwamitin ga majalisar, ya ce amincewar da majalisar ta yi […]
Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da bukatar da gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar mata na neman ciwo bashin Naira biliyan 20 domin aiwatar da wasu ayyuka a jihar.
Shugaban kwamitin kudi na majalisar, Alhaji Abubakar Zakari wanda ya gabatar da rahoton kwamitin ga majalisar, ya ce amincewar da majalisar ta yi zai bai wa gwamnatin jihar damar gudanar da wasu muhimman ayyuka da za su kara bunkasa jihar.
Sannan majalisar dokokin ta jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta mika mata karin kasafin kudin ta domin yin nazari a kai domin ingantuwar aiki, tare da yin kira ga gwamnatin da ta yi kyakkyawan aiki da kudin da ta ranta domin bunkasa jihar.
Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne gwamna Ganduje ya aike da takardar neman amincewar majalisar domin ta ciwo bashin Naira biliyan 20 domin ta yi wasu ayyuka ciki har da biyan ’yan fensho da ma’aikatan kwashe shara da kuma sauran aikace-aikace na kyautata rayuwar al’uma.