Majalisa ta ba da umarnin a tsare Gwamnan CBN da Akanta-Janar
Majalisar Tarayya ta ba da umarnin tsare Gwamnan Bankin CBN, Olayemi Cardosa da kuma Akanta-Janar na Kasa Oluwaoyin Madein.
Majalisar Tarayya ta ba da umarnin tsare Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardosa da Akanta-Janar na Kasa Oluwaoyin Madein.
Kwamitin Karbar Korafi na Majalisar ne ya ba da umarce tsare da wasu kamfanonin mai 15 kan kin amsa gayyatarsa domin amsa tambayoyi kan bangaren albarkatun man Najeriya,
Kwamitiin majalisar ya ba da umarnin ne da murta daa baan samun korafi daga wani mai suna Fidelis Uzowanem a ranar Talata.
Sauran wadanda umarnin ya shafa su ne Kamfanin Kula da Zuba Jarin Mai na Kasa (NAPIM) da kamfanonin hakar danyen mai na Total da Shell da Agip da Pan Ocean Oil da Newcross E&P da kuma Frontier Oil.
Sauran su ne Ethiop Eastern Exploration and Production da Western Africa Exploration and Production.
- ’Yan bindiga sun sumar da basaraken Abuja da duka kan rashin cikar kudin fansa
- Ba za mu yafe jinin masu Mauludi da sojoji suka kashe ba —Sheikh Jingir
Aminiya ta ruwaito cewa majalisa ta saba irin wannan barazana, kasancewar kundin tsarin mulki a ba ta hurumin tilasta duk wanda a kamata, ya hallara a gabansu domin amsa tambayoyi.
Irin haka na faruwa ne kuma idan wadanda aka aike wa goron gayyata ba su so ba.
Galibi mambobin majalisar sun fi so shugaban hukuma ma’aikatar da abin da take dubawa ya zo da kansa ba bisa wakilci ba.
Wakilinmu a ruwaito cewa awanci a zaman majalisar ko kwamitocinta batutuwa da awa ne kan taso kan al’amura don haka suka bukatar amsa daga shugaban hukuma ko ma’aikatar da lamarin ya shafa.
Sai dai a lokuta da dama shugabannin da ake gayyata suka aiko da wakilansu ne, wanda majalisar ba ta jin dadin haka, kuma take kallon haka a matsarin rashin mutunta ta.