Majalisa ta ba da wa’adin nemo ɓata-garin da suka kashe sojoji a Delta
Majalisar ta ce abin akwai ta da hankali kwarai sosai yadda ɓata-garin suka hallaka sojojin.
Majalisar Wakilai ta bayar da wa’adin mako hudu na tabbatar da an nemo wadanda suka kashe sojojin Najeriya 17 a Jihar Delta.
An yi wannan kira ne bayan wani dan majalisar, Babajimi Benson daga Jihar Legas ya gabatar da kudirin gaggauta nemo bata-garin da suka kashe sojojin a ranar Alhamis.
Majalisar wadda ta bayyana takaici, ta bai wa rundunar sojin kasar umarnin nemo wadanda suka aikata wannan mummunan al’amari ga dakarun da ke bakin aiki.
- Magidancin da ke tafiyar kilomita 9 domin karɓo sadakar abincin buɗa baki
- Tudor ya maye gurbin Sarri a matsayin kocin Lazio
Babajimi Benson ya ce, “abin akwai ta da hankali kwarai sosai yadda ɓata-garin suka hallaka sojojin.
“Sojojin nan da aka kashe fa sasanci za su yi tsakanin jama’ar Okoloba da na Bomadi na Jihar Delta, amma aka kasashesu. Sannan bayan an kashesu kuma aka farke kirjinsu aka ciri zukatansu da wasu sassan jikinsu. Dole ne a hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
“Idan ba a dauki matakin gaggawa kuma na gaske ba, to lallai za a sanyaya guiwar zaratan sojojinmu da ke kokarin kare rayuwarmu dare da rana.”
“Binciken mu ya gano cewa shugaban wannan runduna da aka hallaka gwarzon soja ne, domin kuwa yana daya daga cikin wadanda suka karbo wasu yankuna da ’yan kungiyar Boko Haram ta yi iko da su a shekarun baya.
Ya ce, waɗannan sojoji da aka hallaka suna kan hanyarsu ta kawo sasanci da fahimtar juna a tsakanin al’ummar Okoloba da ke Ughelli ta Kudu da kuma na Karamar Hukumar Bomadi a Jihar Delta.
Bayan muhawarar ce majalisar ta bukaci kwamitinta mai lura da ayyukan rundunar sojin kasar da su hada kai da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar cewa an yi duk mai yiwuwa wajen hukunta wadannan mabarnata nan da mako hudu.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne dai aka shiga farautar ɓata-garin da suka kashe dakaru 17 da ke aiki da bataliya ta 181 a Karamar Hukumar Bomadi a Jihar Delta.
Daga cikin wadanda ɓata-garin suka kashe, har da kwamandan da ke jagorantar sojojin da wasu masu mukamin Manjo biyu da wani mai mukamin kyaftin ɗaya, sai kuma kananan sojoji 12 da suke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.