Majalisa ta bayar da umarnin rufe kamfanin fasa dutse a Bunkure

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayar da umarnin rufe wani kamfanin fasa duwatsu da ke gudanar da aiki a yankin Qaramar Hukumar Bunkure. Bayar da umarnin da majalisar ta yi ya biyo bayan gabatar da qudurin gaggawa da dan majalisar yankin mai wakiltar qaramar hukumar ta  Bunkure, Honarabul Muhamamd Uba Gurjiya ya gabatar a gaban […]

Majalisa ta bayar da umarnin rufe kamfanin fasa dutse a Bunkure

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayar da umarnin rufe wani kamfanin fasa duwatsu da ke gudanar da aiki a yankin Qaramar Hukumar Bunkure.

Bayar da umarnin da majalisar ta yi ya biyo bayan gabatar da qudurin gaggawa da dan majalisar yankin mai wakiltar qaramar hukumar ta  Bunkure, Honarabul Muhamamd Uba Gurjiya ya gabatar a gaban majalisar.

Honarabul Uba Gurjiya ya shaida wa majalisar irin qalubalen da al’ummar yankinsa ke fuskanta game da ayyukan kamfanin farfasa duwatsun, inda ya ce tuni wasu suka sami raunuka baya ga wadanda ya rasa ransa dungurum-gum.

Har ila yau dan majalisar ya bayyana cewa al’ummar yankin sun kamu da cututtukan da suka shafi maqwagoro sakamakon qura da ke tashi a koyaushe da kamfamin ke gudanar da ikinsa a garin, inda wasu tuni suka sami cutar asma da sauransu.

Honarabul Gurjiya ya bayyana cewa akwai kuma da dama daga cikin al’ummar yankin da aikin na fasa duwatsun ya yi sanadiyyar rushewar gidajensu.

Da yake bayar da waccan umarni, Shugaban Majalisar, Honarabul Yusuf Abdullahi Atta ya kuma ce majalisar za ta gurfanar da kamfanin gaban kotu don amsa tuhumar gudanar da aiki ba tare da iznin hukuma ba, haka kuma don neman haqqin mutanen da aka rugurguza musu gidaje da kuma wadanda suka kamu da cututtuka a yayin gudanar da aikin fasa duwatsun.

Da yake yi wa manema labarai qarin bayani game da lamarin, dan majalisar ya bayyana cewa ba za su yi qasa a gwiwa ba wajen karbo haqqoqin dukkan masu haqqi daga kamfanin. “Akwai wadanda suka kamu da cututtukan asma da sauransu da kuma wanda ya rasa ransa a lokacin da yake gudanar da wannan aiki. Akwai  kuma wasu da suka sami raunuka wadanda ya kamata a biya su haqqinsu, amma ba a biya su ba. Za mu nemo dukkan haqqoqin wadannan al’umma tamu a gaban kotu.”

dan majalisar ya kuma gode wa al’ummar yankin bisa zurfin tunani da haquri da suka yi na qin daukar doka a hannunsu, a maimakon haka suka yi tunanin sanar da hukuma don daukar matakin da ya dace.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno