Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Majalisar ta amince da ƙudirin kawo ƙarshen sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’addan.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Majalisar Dattawa ta buƙaci dakarun sojin Najeriya, su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a jihohin Sakkwato da Kebbi don kawo ƙarshen ƙungiyar ‘yan ta’adda ‘Lakurawa’

Wannan ya biyo bayan wani ƙudirin gaggawa da Sanata Yahaya Abdullahi (PDP-Kebbi) ya gabatar.

Ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar, wadda ta fito daga ƙasashen Burkina Faso da Mali, ta shigo Najeriya ta iyakar Nijar.

A baya-bayan nan, ƙungiyar ta kai wa wasu yankuna hari ciki har da ƙauyen Mera a Jihar Kebbi.

Majalisar ta yaba wa sojoji kan martanin gaggawa da suka bayar, tare da shawartar su da su haɗa kai da al’ummomi da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro.

Har ila yau, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aike tawaga don tantance irin ɓarnar da da Lakurawa duka yi tare da bai wa waɗanda lamarin ya shafa agaji.

Sanata Abdullahi da Sanata Adamu Aliero sun jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa domin hana ƙungiyar yaduwa zuwa wasu sassan ƙasar nan.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya goyi bayan ƙudirin, inda ya yi gargaɗin cewa gaza ɗaukar matakin na iya ƙara yaɗuwar ta’addanci a sassan Najeriya.