Majalisa ta bukaci a taka wa masarautar Dutse birki a kan karin gunduma

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta nemi gwamnatin jihar ta taka wa masarautar Dutse birki wajen hana ta kirkiro gundumar hakimi a Harbour Sabuwa ko dauke Hakimin Harbour Tsohuwa zuwa Harbour Sabuwa.Da yake karanta rahotonsa ga majalisar shugaban kwamitin binciken rikicin da ya auku a yankin Musa Sule Dutse ya ce hakan ne ya haifar da […]

Majalisa ta bukaci a taka wa masarautar Dutse birki a kan karin gunduma
Majalisa ta bukaci a taka wa masarautar Dutse birki a kan karin gunduma

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta nemi gwamnatin jihar ta taka wa masarautar Dutse birki wajen hana ta kirkiro gundumar hakimi a Harbour Sabuwa ko dauke Hakimin Harbour Tsohuwa zuwa Harbour Sabuwa.
Da yake karanta rahotonsa ga majalisar shugaban kwamitin binciken rikicin da ya auku a yankin Musa Sule Dutse ya ce hakan ne ya haifar da matsalar da aka samu mutuwar daya da ji wa jama’a da dama rauni.
Ya ce kwamitin ya ziyarci marasa lafiya da ke kwance a asibitoci don jajantawa kuma ya ziyarci dagatai da masu unguwanni don jajanta wa jama’ar yankunan biyu.  
Kwamitin ya bukaci majalisar ta sanar da gwamnatin jihar bukatar ta taka wa masarautar Dutse birki kan kokarinta na dage hakimin daga Harbour Tsohuwa zuwa Harbour Sabuwa, kuma ta dakatar da komai kan batun har sai zaman lafiya ya dawo a yankin.