Majalisa ta bukaci Buhari ya gaggauta bayyana gabanta
Majalisar Wakilai ta Tarayya ta nemi Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gaggauta bayyana a gabanta, domin yin bayani dangane da tabarbarewar tsaro wanda ke haddasa munanan kashe-kashe da ke ta faruwa a kasar nan. Majalisar ta amince da wannan roko ne, bayan da dan Majalisa mai wakiltar Ungogo da Minjibir daga Jihar Kano, Honarabul Bashir […]

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta nemi Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gaggauta bayyana a gabanta, domin yin bayani dangane da tabarbarewar tsaro wanda ke haddasa munanan kashe-kashe da ke ta faruwa a kasar nan.
Majalisar ta amince da wannan roko ne, bayan da dan Majalisa mai wakiltar Ungogo da Minjibir daga Jihar Kano, Honarabul Bashir Baballe na APC, ya gabatar da rokon kudirin da dan Majalisa daga Benuwai, Mark Gbilah, shi ma dan APC ya bagatar.
Majalisar ta amince da kudirin da Gbilah ya gabatar, a kan harin da sojoji suka kai a garin Naka, inda suka banka wa kusan rabin garin wuta, saboda matasan garin sun yi wa wani soja kisan-rubdugu.
Daga nan kuma ‘yan majalisar suka amince da cewa shugabannin hukumomin tsaron kasar nan sun gaza, kuma ba za su iya magance matsalar tsaro a kasar nan ba. Don haka sun nemi Shuga Buhari da ya tsige su, sannan ya gaggauta maye gurbinsu da wasu da masu nagarta da cancanta.
Haka zalika majalisar ta jingine zamanta na kwanaki uku, domin nuna jimami da kuma alhini bisa jama’ar da ake ta kashewa bila adadin a fadin kasar nan. Sun kuma nemi gwamnatin tarayya ta shelanta cewa makiyaya masu kashe mutane su ma ‘yan ta’adda ne, kuma sun nemi a yi wa kowane makiyayi rajista.