Majalisa ta bukaci gwamnati ta kafa hukumar kayyade farashin kayayyaki

Majalisar ta ce yin hakan zai rage yawan tashin farashin kayayyaki babu dalili

Majalisa ta bukaci gwamnati ta kafa hukumar kayyade farashin kayayyaki

Kakakin Majalisar wakilai Tajudeen Abbas

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta kirkiri hukumar kayyade farashin kayayyaki don dakile hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan.

Bukatar ta biyo bayan amincewa da kudurin al’umma da dan majalisa Hussaini Muhammad Jalo ya gabatar a zauren majalisar a yayin zamanta na ranar Alhamis.

Da yake gabatar da kudurin, dan majalisar ya ce kafa hukumar zai taka muhimmiyar rawa wajen magance yawan tashin gwauron zabin da kayayyaki suke yi sanadiyyar tashin farashin man fetur da karyewar darajar Naira.

Daga nan sai ya bukaci majalisar da ta bukaci Ma’aikatar Ciniki da Kasuwanci da ta duba yiwuwar yi wa kudurin dokar garambawul da nufin kafa sabuwar hukumar.

Hussaini Jalo ya kuma ce hukumar za ta rika sanya idanu kan farashin albarkatun man fetur sannan ta tabbata dillalan shi ba sa fakewa da farashin man a kasuwannin duniya wajen tsuga masa kudi a cikin gida.

Daga nan ne sai majalisar ta amince da kudurin, sannan ta mika shi ga kwamitinta na kasuwanci domin daukar mataki na gaba.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda