Majalisa ta bukaci sojoji su saki shugaban Miyetti Allah
Majalisar Wakilai ta umarci Rundunar Sojin Najeriya ta gaggauta sakin Alhaji Bello Bodejo, tare da ba shi hakuri kan tsare shi ba bisa ka’ida ba
Majalisar Wakilai ta umarci Runduna Sojin Najeriya ta gaggauta sakin Alhaji Bello Bodejo, wanda suke tsare da shi tun a makon jiya.
A zamanta na ranar Talata, majalisar ta umarci Babban Hafsan Tsaron Nijeriya da kuma Babban Hafsan Sojin Kasa na Nijeriya su umarci Kwamandan Runduna ta 177 da ke tsare da Bello Bodejo da ya gaggauta sakin sa, tare da ba da hakuri kan tauye hakkinsa.
Sannan ta umarci manyan hafsohjin sojin da su bayyana a gaban kwamitinta na kare hakkin dan Adam ranar Juma’a domin amsa tambayoyi kan dalilin da sojoji ke tauye hakkin Bello Bodejo.
Majalisar ta yanke wannan hukunci ne bayan dan Malajisa Mansur Manu Soro ya gabatar da lamarin yana mai yin tir da tsare Bello Bodejo da sojoji suka yi tsawon mako guda ba tare da umarnin kotu ko gayyatar shugaban Fulanin ba.
- Gwmanati ta ware N263bn don gina tashoshin lantarki a Sakkwato da wasu 4
- ’Yan Yahoo 159 ’yan kasar waje da ’yan Nijeriya 599 sun shiga hannun EFCC a rana guda
Alhaji Bello Bodejo, shi ne Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore, kuma sojojin Runduna ta 177 da ke Keffi a Jihar Nasarawa ne suka yi awon gaba da shi daga gidansa.
Sojoji sun kama shi ne bayan wani rikici da aka samu tsakanin tsakanin wani tsohon Janar din soja da mazauna yankin Maliya, inda Shugaban na Miyetti Allah yake zaune tare da iyalansa.
Dan Malajisa Mansur Manu Soro ce dokar kasa ta takaita aikin sojoji ne ga tsaron kasa daga masu kutse daga kasashen waje da ’yan ta’adda da ke neman barazana ga kasa.
Majalisar ta yi Allah wadai da tsare Bello Bodejo na mako guda ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, da kuma yadda sojoji suka tsoma baki a rikicin da ke tsakanin al’umma.