Majalisa ta fara muhawara kan kudurin dokar Mulkin Karba-karba

Majalisar Dattawa ta fara muhawara kan kudurin kafa dokar mulkin karba-karba tsakanin shiyyoyin siyasar Najeriya.

Majalisa ta fara muhawara kan kudurin dokar Mulkin Karba-karba

Majalisar Dattawa

Majalisar Dattawa ta fara muhawara kan kudurin dokar mulkin karba-karba tsakanin shiyyoyin siyasar Najeriya.

A farkon shekarar 2022 da muke ciki ne Majalisar ta kammala karatu na farko kan kudurin dokar wanda Sanata Abba Moro a gabatar.

Wannnu batu na neman yin dokar mulkin karba-karba dai ya janyo ce-ce-ku-ce, kamar yadda batun mulkin karba-karba ya jima yana tayar da kura a fagen siyasar Najeriya.

Wasu ’yan Majalisar Dattawa na ganin dokar za ta bai wa al’ummomi, musamman marasa rinjaye damar shiga a dama da su a fagen shugabancin kasar nan.

Wasu takwarorinsu kuma na zargin kafa dokar za ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.

A lokacin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci wanda ya gabatar da kudurin da ya janye ta, ya je ya yi masa kwaskwarima sannan ya sake gabatar wa majalisar.