Majalisa ta janye dakatarwar da ta yi wa Abdulmini Jibrin
A ranar Talatar da ta gabata ce Majalisar Wakilai ta janye dakatarwar da ta yi wa Alhaji Abdulmunin Jibrin daga Jihar Kano. Hakan ya biyo bayan wata wasika ce da ya rubuta ya aike wa majalisar yana ba ta hakuri. Duk da dai ba a karanta wasikar a zauren majalisar ba, amma Shugaban Majalisar, Yakubu […]

A ranar Talatar da ta gabata ce Majalisar Wakilai ta janye dakatarwar da ta yi wa Alhaji Abdulmunin Jibrin daga Jihar Kano. Hakan ya biyo bayan wata wasika ce da ya rubuta ya aike wa majalisar yana ba ta hakuri.
Duk da dai ba a karanta wasikar a zauren majalisar ba, amma Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara ya ce Jibrin ya rubuto takarda yana ba da hakuri, kuma ya cika sharuddan da suka kamata a mai da shi majalisa, kuma har ya samu damar shiga majalisar a shekaranjiya Laraba.
An dakatar da Abdulmumin Jibrin, wanda ke wakiltar kiru da Bebeji daga Jihar Kano ne tun cikin shekarar 2017, bayan da aka cire shi daga Shugabancin Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar bisa zarginsa da hannu a badakalar da ta dabaibaye kasafin kudin shekarar.
Sannan aka maye gurbinsa da Mustapha Bala Dawaki daga Kano, wanda a baya shi ne Shugaban Kwamitin Gidaje na Majalisar. Matakin ya tunzura dan majalisar, inda ya rika yin tonon silili a kanta tsawon lokaci kafin daga bisani aka daina jinsa.