Majalisa ta karyata yunkurin tsige Gwamnan Yobe
Majalisar Dokokin Jihar Yobe ta karyata jita-jitar da ta ce wasu ’yan adawa ke watsawa cewa ’yan majalisar sun yi zama na musamman a kasar Saudiyya a cikin watan Ramadan da nufin tsige Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam daga kujerarsa.Bayan zaman da ta yi a ranar Talata majalisar ta musanta wannan jita-jita, inda shugabanmajalisar Alhaji […]
Majalisar Dokokin Jihar Yobe ta karyata jita-jitar da ta ce wasu ’yan adawa ke watsawa cewa ’yan majalisar sun yi zama na musamman a kasar Saudiyya a cikin watan Ramadan da nufin tsige Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam daga kujerarsa.
Bayan zaman da ta yi a ranar Talata majalisar ta musanta wannan jita-jita, inda shugaban
majalisar Alhaji Adamu Dala Dogo ya bayyana wa Aminiya cewa, maganganun da wasu ke yadawa cewa wai ’yan majalisar na shirin tsige Gwamna Gaidam daga kan kujerarsa ba komai ba ne illa maganar ’yan adawa musamman ’ya’yan Jam’iyyar PDP.
Ya ce bakin ’yan majalisar duk ya zo daya wajen yin Allah wadai da masu yada irin wannan jita-jita kuma ya tabbatar wa jama’ar Jihar Yobe cewa kudi ba zai taba rudinsu su bar tafarkin da suke a kai na biyayya ga Jama’iyyar APC ba, “Mu ba kudi ba ne a gabanmu abin da ke gabanmu shi ne tallafa wa Gwamna Gaidam don ciyar da Jihar Yobe gaba ta wajen gudanar da ayyukan raya kasa, kuma ko yanzu tubarkallah,” inji shi.
Shugaban ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba da goyon bayansu ga Gwamna Ibrahim Gaidam a zabe mai zuwa don sake komawa kan kujerar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyarsu ta APC.
Ya cew, masu yada wannan jita-jita su sani cewa ’yan majalisar sun sha bamban da takwarorinsu na Adamawa da Nasarawa, a kullum suna goyon bayan gaskiya ne.
Tun farko da yake mika wannan kudiri na yin watsi da jita-jitar a gaban majalisar, dan majlisar mai wakiltar Bade ta Tsakiya, Injiniya Siraja Wakil ya nemi ’yan majalisar ne su goyi bayan kudiri nasa na yin watsi da jita- jitar tare da goya baya ga Gwamna Ibrahim Gaidam.