Majalisa ta ki yarda a biya matasa tallafin naira 5,000

A shekaranjiya Laraba ne Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudurin dokar da ta bukaci gwamnatin tarayya ta rika bai wa matasan da ba su da ayyukan yi tallafin naira 5,000 kowane wata.Yawancin sanatocin da suka ki amincewa da kudurin ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne. Yayin da takwarorinsu na jam’iyyar adawa ta PDP suka […]

Majalisa ta ki yarda a biya matasa tallafin naira 5,000
Majalisa ta ki yarda a biya matasa tallafin naira 5,000

A shekaranjiya Laraba ne Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudurin dokar da ta bukaci gwamnatin tarayya ta rika bai wa matasan da ba su da ayyukan yi

tallafin naira 5,000 kowane wata.
Yawancin sanatocin da suka ki amincewa da kudurin ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne. Yayin da takwarorinsu na jam’iyyar adawa ta PDP suka goyi bayan kudirin, sai dai ba su samu cikakken goyon bayan da zai sa a amince da bukatar ba.
Sanata Mai Wakiltar Babban Birnin Tarayya, Philip Aduda na jam’iyyar PDP ne ya gabatar da kudirin a zauren majalisar. Kuma ya ce ya yi hakan ne saboda matsin tattalin arziki da marasa aikin yi suke fuskanta a halin yanzu.
Jam’iyyar APC ta yi alkawarin bai wa matasan da ba su da ayyukan yi naira 5,000 a duk wata, a lokacin da take yakin neman zabe.
Masana dai suna ganin cewa da wuya ta iya cika wannan alkawarin saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin da kasar ke ciki, inda ko makon jiya Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake wata ziyara a kasar Indiya, ya ce kasar nan ta talauce.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno