Majalisa ta kori kudurin hana hafsoshin tsaro karkatar da kudade

Akasarin sanatoci sun ki amincewa da kudirin da Adams Oshiomhole ya gabatar.

Majalisa ta kori kudurin hana hafsoshin tsaro karkatar da kudade

Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudirin da ke neman hana manyan hafsoshin tsaro karkatar da kudaden da aka ware wa bangaren.

A ranar Laraba sanatoci suka kada kuri’ar kin amincewa da kudirin, wanda ke neman wajabta wa shugabannin tsaro gudanar da kudaden da ke karkashin kulawarsu domin samar da makamai da sauran kayan aikin tsaro kadai.

Sanata Adams Oshiomhole ne ya gabatar da kudirin a lokacin da yake tsokaci kan kudirin da Sanata Ali Muhammad Ndume ya gabatar kan harin kunar bakin wake da Boko Haram ta kai a garin Gwoza a karshen mako.

Oshiomhole ya bukaci majalisar ta umarci kwamitocinta na sojin kasa da sojin sama da kuma sojin ruwa su tsananta sa ido kan manyan shugabannin tsaro.

Ya ce ya kamata kwamitocin su rika sa ido tare da tabbatar da cewa sayen makamai da sauran kayan tsaro da aka ware kudade domin su ne aka yi amfani da kudaden a kansu.

Ya ja hankalin sanatoci cewa rashin hakan ne ya sa shugabannin tsaro suka karkatar da kudaden da aka ware wa bangaren, suka gina jami’a, maimakon ainihin abin da aka ware wa kudaden.

Sai dai bukatar tasa ba ta samu shiga ba, duk da cewa Sanata Imasuen Neda, ya goyi bayan kudirin.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya gabatar da batun ga zauren majalisar domin kada kuri’a, amma marasa goyon baya suka samu yi rinjaye.