Majalisa ta nemi a haramta amfani da robobin ‘tekawe’ a Najeriya

Majalisar Wakilai ta bukaci a haramta amfani da robobin cin abinci na ‘tekawe’ da ba sa rubewa saboda barazar da suke ga lafiyar al’ummar

Majalisa ta nemi a haramta amfani da robobin ‘tekawe’ a Najeriya
Majalisar Wakilai ta bukaci a haramta amfani da robobin cin abinci na ‘tekawe’ da sauransu da ake amfani da su sau guda.

Majalisar ta ce haramta robobin wadanda ba sa rubewa na da muhimmanci domin kare muhalli da kawar da cututtuka masu alaƙa da sinadaren da robobin ke dauke da su.

Dan majalisar Muktar Shagaya ne ya gabatar da kudirin inda ya jaddada alhakin da tsarin mulki ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya na kare rayuwar al’umma da kuma muhalli.

Styrofoam da robobi da ake amfani da sau ɗaya kacal na haddasa toshewar hanyoyin ruwa, gami da lalata kasar noma da kuma ingancin iska.

Bugu da ƙari, ana danganta sinadaran styrofoam da haifar da cututtuka da irin su ciwon daji, yawan mantuwa, rashin hangen nesa da rashin ji, lalurar ƙwaƙwalwa da sauransu.

Kasashe da dama, da suka hada da Taiwan da Ruwanda da Ingila da kasashen Turai, sun riga sun haramta styrofoam.

Wasu jihohin Amurka ma sun dauki irin wannan matakin, haka ma jihohin Legas da Abia a Najeriya.

Majalisar wakilai ta amince da cewa akwai wasu hanyoyi da  abubuwan da za su maye gurbinsa da za a iya amfani da su fiye da sau guda, wanda hakan na iya rage gurbacewar muhalli da haɗarin lafiya da ke da alaƙa da robobin.

Gaggawar daukar matakin ya samo asali ne daga karuwar amfani da styrofoam da robobin da ake amfani da su sau daya a Najeriya.

Lamarin ba wai kawai yana kara ta’azzara sharar robobi da gurbacewar muhalli ba, har ma yana kawo illa ga lafiyar jama’a.

Yayin da take kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki mataki, Majalisar ta ba da shawarar aiwatar da tsarin da aka tsara a hankali.

Hakan zai ta taimaka wajen kawar da abubuwa masu cutarwa tare da kiyaye albarkatun kasa, muhallin Najeriya, da jin dadin ‘yan kasa.

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe