Majalisa ta sahale wa Tinubu ranto dala miliyan 516.3

Duk da cewa bashin zai ƙara yawan jimillar wanda ake bin Najeriya a halin yanzu, zai taimaka matuƙa waje bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Majalisa ta sahale wa Tinubu ranto dala miliyan 516.3

Majalisar Dattawan Najeriya ta sahale wa Shugaba Bola Tinubu, karɓo bashin dala miliyan 516.3 domin gudanar aikin hanyar Sakkwato zuwa Badagry.

Hakan ya biyo bayan buƙatar da shugaban ya aike a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun 2026, wadda ya nemi amincewar majalisar domin ranto kuɗin.

Aminiya ta rawaito cewa buƙatar ta biyo ta hannun Kwamitin Rance na Cikin Gida da Waje ne tun a ranar 23 ga watan Afrilu, wanda ya gabatar da rahoton ga majalisar, ya kuma bayar da shawarar amincewa da buƙatar.

Da yake gabatar da rahoton a madadin shugaban kwamitin, Adamu Aliero, ya ce aikin ya kai nisan kilomita 1,000 daga Sakkwato zuwa Badagry da ke Jihar Legas.

Ya kuma ce za a gudanar da aikin ne domin ƙarfafawa da kuma sada jihohin Sakkwato, Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Ogun da Legas cikin sauƙi.

Haka kuma ya kamanta aikin a matsayin wanda zai kawo gagarumin ci gaba a fannin kasuwanci da kuma samar da sufuri mai inganci.

Ya ƙara da cewa, hakan zai rage doguwar tafiya, da rage kuɗaɗen kai wa da kawowa ga jama’a, baya ga kawo ci gaba a fannin noma da kiwo da kuma kasuwanci.

Rahoton kwamitin ya kuma ce shirin samar da kuɗin aikin ya rataya ne a wuyan wani banki na ƙasar Jamus da tallafin Ma’aikatar Inshorar hannun jari ta Musulunci da Bashin Fitar da Kayayyaki.

Ya ce duk da cewa bashin zai ƙara yawan jimillar wanda ake bin Najeriya a halin yanzu, zai taimaka matuƙa waje bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

A hannu guda kuma, Sanatan Borno ta Arewa ya ce aikin zai rage matsalar rashin aikin yi da taɓarɓarewar tsaro, yayin da mataimakin shugaban majalisar, Barau Jibrin ya ce zai taimaka wajen sada Kudanci da Arewacin Najeriya cikin sauƙi.

A ƙarshe dai shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya nemi ji ta bakin sauran ‘yan majalisun, waɗanda kuma suka amince da shi.