Majalisa ta soke harajin tura kudi ta intanet

Majalisa ta ce babu dalilin kirkiro da wani haraji alhali al’ummar kasa suna cikin matsin rayuwa sakamakon janye tallafin mai da na wutar lantarki

Majalisa ta soke harajin tura kudi ta intanet

Majalisar Dokoki ta Kasa

Majalisar Wakilai ta soke harajin tsaron intanet da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna su rika karba daga daidaikun mutane da ke aika kudi ta intanet.

Majalisar ta umarci CBN ta kuma umarci CBN ya gagguta janye umarnin da ya ba wa bankuna na cirar harajin na kaso 0.5% daga kudaden da aka tura ta na’urorin zamani.

Umarnin majalisar na zuwa ne bayan koke da kakkausar suka da sabuwar dokar ta CBN ke sha daga ’yan Najeriya da kanfanoni da masana da ma kungiyoyi.

Tun bayan bullar sanarwar CBN ya ranar Lahadi ’yan Najeriya suke kokawa da ganin bankuna sun fara cirar harajin, musamman yadda suke bayyana hakan a matsayin rashin tausaya wa halin da ake ciki na matsin rayuwa a kasar.

Aminiya ta ruwaito a baya cewa majalisar ta dakatar da sauraron kudirin ne soke sabuwar dokar ta CBN, wanda dan majalisa Mansur Manu Soro ya gabatar.

Bayan gabatar da kudirin nasa a ranar Laraba sai shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen, ya jingine maganar da cewa shugabancin majalisar zai tattauna a kai.

Da yake gabatar da kudirin a ranar Alhamis, Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda, ya ce babu hujjar kafa wata dokar karbar haraji, alhali ’yan Najeriya na fama da matsananciyar rayuwa a sakamakon janye tallafin mai da na wutar lantarki.

Hasali ma majalisar ta yi wa Dokar tsaron intanet mummunar fahimta, domin dokar ta riga ta ayyana wadanda harajin ya hau kansu.

Don haka ta umarci kwamitin majalisar kan harkokin bankuna da dangoginsu da ya dora CBN a kan hanya a game da dokar da babban bankin ya yi wa gurguwar fahimta.

A cewarta, wadanda dokar harajin ta hau kansu su ne; bankuna, cibiyoyin hadahadar kudade, kamfanonin inshora, kamfanin intanet, kamfanonin sadarwa, da kuma kasuwar hadadar hannayen jari ta Najeriya.

Dokar yaki da laifuka ta intanet ta tanadi cewa za a ciri harajin kaso 0.5% a kan duk kudaden da wadannan cibiyoyin suka tura ta intanet, a tuwa ga CBN.

CBN ne zai adana kudaden harajin, wadanda da su za gudanar da asusun kasa na samar da tsaro ta intanet da ke karkashin ofishin mashawarcin shugaban kasa kan tsaro (ONSA).

To sai dai sabon umarnin CBN ya sa bankuna sun fara cirar harajin daga daidaikun mutane, lamarin da ya harzuka jama’ar kasar.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa