Majalisa ta tabbatar da naɗin Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalan Najeriya
Kekere-Ekun ce babbar jojin Nijeriya ta 23 kuma mace ta biyu da ta taba hauwa wannan mukami.
Majalisar Dattawa a wannan Larabar ta tabattar da naɗin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya.
Hakan na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawan wasiƙa a jiya Talata, yana buƙatar a tabbatar da Kekere-Ekun a matsayin Babbar Jojin Najeriya.
- Sake naɗa Sanusi Sarkin Kano ya fi komai daɗi a wajena — El-Rufai
- TY Danjuma Ya Bayar da Tallafin N1bn Kan Ambaliyar Maiduguri
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar a zauren majalisar a jiya Talata.
Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwarsa game da zaɓenta da aka yi sannan ya buƙaci majalisar ta gaggauta ɗaukar mataki akai.
Kudirat Kekere-Ekun ta kasance Alƙalin Alƙalan Nijeriya ta riƙo tun daga watan Agusta bayan da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya daga matsayin.
A watan Agustan ne Hukumar Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta bai wa Shugaba Tinubu shawarar naɗa Mai Shari’a Kekere-Ekun a matsayin wacce za ta gaji Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.
Bayan tambayoyi da kuma tantancewa, a ƙarshe Majalisar Datttawan ta tabbatar da naɗin Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalai ta Nijeriya.
A lokacin da take bayani gaban majalisar, Mai Shari’a Kekere-Ekun ta ce za ta rungumi aiki da fasahar zamani a ayyukan shari’a a Nijeriya.
Alƙalan Kotun Koli da na Daukaka Kara na cikin waɗanda suka raka Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun Majalisar Dattawan domin tantance ta.
A yanzu Kekere-Ekun ita ce babbar jojin Nijeriya ta 23 kuma mace ta biyu da ta taɓa hawa wannan mukami.
Mace ta farko da ta hau kan wannan mataki ita ce Mai Shari’a Maryan Aloma Mukhtar, wacce ta rike mukamain Alƙalin Alƙalan Nijeriya tsakanin watan Yulin 2012 da Nuwambar 2014.