Majalisa ta tantance Ministoci 24 saura 19

A yau Alhamis Majalisar Dattawa ta tantance sunaye 14 da aka mika mata don zama Ministocin Najeriya, wanda ya kama a yanzu haka an tantance sunaye 24 cikin 43 da Shugaba Buhari ya bukaci su zama Ministocinsa, sauran sunaye 19. Sunayen da aka tantance a yau sun hada da: SanataTayo Alasoadura (Ondo), Abubakar Aliyu (Yobe), […]

Majalisa ta tantance Ministoci 24 saura 19

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan

A yau Alhamis Majalisar Dattawa ta tantance sunaye 14 da aka mika mata don zama Ministocin Najeriya, wanda ya kama a yanzu haka an tantance sunaye 24 cikin 43 da Shugaba Buhari ya bukaci su zama Ministocinsa, sauran sunaye 19.

Sunayen da aka tantance a yau sun hada da: SanataTayo Alasoadura (Ondo), Abubakar Aliyu (Yobe), Mustapha Shehuri (Borno), Manjo Janar Bashir Magashi (Kano) , Zuibaru Dada (Niger) da Timipre Slyva (Bayelsa)

Sauran su ne: Ramatu Aliyu (Kogi), Niyi Adebayo (Ekiti), Mohammed Abdullahi (Nassarawa), Sunday Dare (Oyo), Muhammadu Bello (Adamawa), Sanata Chris Ngige (Anambra) da Sadiya Umar-Farouk (Zamfara).