Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji
Ƙudirin kafa dokokin haraji guda huɗu da Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar sun tsallake karatu na biyu.

Zauren Majalisar Wakilai
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji.
Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi.
- Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano
- Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi
Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na biyu.
Wannan zaman sauraron ra’ayin da za a gudanar zai ba da damar karɓar shawarwarin masu ruwa da tsaki domin ji daga gare su dangane da ƙudirin Dokar Harajin da aka riƙa kai ruwa na a kai a faɗin ƙasar.
Idan ba a manta ba, a farkon watan Janairun da ya gabata ne gwamnonin Nijeriya suka fitar da sabon tsari na rabon haraji a ƙasar, bayan wata ganawa da suka yi da kwamitin da aka kafa domin yin nazari kan ƙudurin sabuwar dokar haraji ta ƙasar.
Tun a ƙarshen shekarar da gabata ce Tinubu ne ya gabatar wa Majalisar Tarayyar ƙudurin aiwatar da gyaran fuska ga dokar harajin, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara da raba kawunan shugabanni a ƙasar.
Haka ne ya kai ga cewa shugaba Tinubu da Majalisar Dokokin Tarayya sun jingine batun muhawara da amincewa da dokar har sai bayan an sake yin nazari a kanta.