Majalisa ta umarci dillalai su ba kamfanonin jirage bashin mai
’Yan Majalisar sun ba da awa 24 a dakatar da sayar wa kamfanonin jirage mai kudi hannu
Majalisar Wakilai ta umarci kamfanonin mai da su gaggauta samar da man jirgin sama ga kamfanonin sufurin jiragen sama ba sai an biya kudi hannu ba.
A zamanta na ranar Laraba, Majalisar ta yi ittifakin sanya baki kan matsakar da karanci da kuma tashin gwauron zabon farashin man jirgin sama cikin sa’a 24, inda ta umarci dillalan man da su yi watsi da tsarinsu na sayar da mai kudi hannu ga kamfanonin sufurin jiragen sama, domin barazana ce ga bangaren.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Wutar Lantarki Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci
- Yadda direba ya yi ajalin daliba a wajen tarbar gwamnan Gombe
’Yan Majalisar sun yanke shawarar ce bayan kudurin da Honorabul Nnolim Nnaji ya gabatar na bukatar “Majalisar ta yi bincike kan karancin man jirgi da tashin gwauron zabon da ya yi, wanda ke barazana ga sufurin jirage sama a Najeriya, yake kuma bukatar Gwamnatin Tarayya ta gaggauta yin wani abu a kai.”
Dan Majalisar ya ce rikicin Rasha da Ukraine ya haifar da rashin tabbas da tashin farashin gangar danyen mai zuwa sama da Dala 125, wanda kuma ya kawo tsadar abubuwan da ake samarwa daga tataccen mai.
Nnaji ya bayyana cewa Najeriya na shigo da man jirgi ne daga kasashen waje, kuma tashin gwauron zabon man babban kalubale ne ga sufurin jiragen sama a kasar.
Ya bayyana cewa an wayi gari a ranar Talata 10 ga Maris, 2022, ana sayar da litar man jirgi a kan N600 a Najeriya, kuma duk da haka da kyar ake samun sa.