Majalisa ta umurci Al-Makura ya dakatar da Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta umurci Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya dakatar da Shugaban Jami’an Jihar da ke Keffi Farfesa Akaro Mainoma bisa zarginsa da cewa bai bi ka’ida ba wajen daukar dalibai a shekarar karatu ta 2015 da 2016 a jami’ar ba. Majalisar ta kuma yi zargin cewa shugaban ya dauki wadanda ba ’yan […]

Majalisa ta umurci Al-Makura ya dakatar da Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa
Majalisa ta umurci Al-Makura ya dakatar da Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta umurci Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya dakatar da Shugaban Jami’an Jihar da ke Keffi Farfesa Akaro Mainoma bisa zarginsa da cewa bai bi ka’ida ba wajen daukar dalibai a shekarar karatu ta 2015 da 2016 a jami’ar ba.
 Majalisar ta kuma yi zargin cewa shugaban ya dauki wadanda ba ’yan jihar ba fiye da ’yan jihar kuma ya kara kudin makaranta ba bisa ka’ida ba.
Shugaban Majalisar Ibrahim Balarabe Abdullahi ne ya bayar da wannan umarni a lokacin wani zaman da majalisar ta yi a Lafiya. Kuma kafin majalisar ta bayar da wannan umarni sai da ta gayyaci Farfesa Mainoma inda ya amsa wasu tambayoyi kan yadda aka samu matsaloli a jerin sunaye da jami’ar ta fitar na daukar dalibanta a shekarar 2015 /2016.
Daga cikin tambayoyi da ’yan majalisar suka yi masa akwai na yawan daliban da aka dauka a kowace karamar hukumar da dalilin da ya sa ya kara kudin makaranta wanda daga ciki har da Naira dubu biyar da kowane sabon dalibi zai biya kafin ya fara karatu da Naira dubu 4 na yi amfani da Intanet da kuma yaya aka yi suka gano’yan jihar daga cikin masu neman shiga jami’ar da sauransu.
Farfesa Akaro Mainoma ya bayyana cewa jami’ar ta bi ka’idar daukar dalibai a shekarar karatu ta 2015/2016, wajen ba ’yan asalin jihar kashi kashe 80 cikin 100 na guraben karatu da kuma kashi 20 ga wadanda ba ’yan asalin jihar ba. Ya kara da cewa bai ga wani abu da zai sa ya debi wadanda ba ’yan jihar fiye da ’yan asalin jihar ba, inda a cewarsa ko a lokacin da yake Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya yana yin iya kokarinsa don tabbatar ’yan Jihar Nasarawa sun samu gurbin karatu a can.
Dangane da sababbin kudin makaranta da ya kara kuwa Farfesa Mainoma ya ce ya yi haka ne da nufin kara wa jami’ar kudin shiga domin ta samu damar gudanar da ayyukan neman ilimi mai inganci.
Majalisar dai ta nuna rashin gamsuwarta da amsoshin inda ta yanke shawarar umurtar Gwamna Al-Makura ya dakatar da shi cikin gaggawa kuma ta nada kwamiti nan take a karkashin Honorabul Daniel Ogah Ogazi don gudanar da bincike a kan lamarin.