Majalisa ta yi ta’aziyar rasuwar lauyan farko a Arewa
Shugabannin Majalisar sun ce rasuwar ta bar gibi mai wuyar cikewa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Kakakim Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, sun mika ta’aziya ga iyalan lauya na farko a Arewacin Najeriya, Alhaji Abdulganiyu Folorunsho AbdulRazaq, mahaifin gwamna Abdulrahman na jihar Kwara.
Lawan da Gbajabiamila sun ce rasuwar tsohon Antoni Janar na Tarayyan kuma Ministan Sufurin Jiragen Kasa a Jamhuriya ta Farko, babban rashi ne ga Najeriya, musamman jihar Kwara da Masarautar Ilorin da iyalan mamacin.
Da suke rokon Allah Ya jikan sa, shugabannin majalisar sun ce Mutawallin na Ilorin wanda ya rasu ranar Asabar ya taka muhimmiyar rawa a dukkanin fannonin rayuwa da ya bayar da gudunmuwa.
A sakonnin ta’aziyar da suka fitar, kowannensu ya ce mamacin ya yi kyakkyawar rayuwa abar koyi kuma ya bar babban gibi mai wuyar cikewa.