Majalisa ta yi watsi da kudurin canja jadawalin zabe

Majalisar Dokoki jiya ta yi watsi da kudurin lokutan zabe wanda shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da shi.   Zaurukan majalisar biyu jiya ba su kula da sabon kudurin ba biyo bayan kin amincewar da shugaban kasar ya yi da gyaran da suka yi wa dokar zaben ta shekarar 2010.   Shugaba Buhari ya […]

Majalisa ta yi watsi da kudurin canja jadawalin zabe

Majalisar Dokoki jiya ta yi watsi da kudurin lokutan zabe wanda shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da shi.
 
Zaurukan majalisar biyu jiya ba su kula da sabon kudurin ba biyo bayan kin amincewar da shugaban kasar ya yi da gyaran da suka yi wa dokar zaben ta shekarar 2010.
 
Shugaba Buhari ya ki amincewa da gyaran fuskar da majalisar ta yi inda ya kafa hujja da dokokin Najeriya.
 
A majalisar, ’yan majalisar sun yanke shawarar su janye tattauna batun sabuwar dokar wacce ake yi mata taken “Kudurin dokar da zai yi gyaran fuskar dokar zabe don bayar da damar yi wa lokutan zaben gyaran fuskar wanda Sanata Sulaiman Nazifi dan jama’iyyar APC daga jihar Bauchi ya dauki nauyi.


Kofin Duniya: Jamus ta lallasa Curaçao da ci 7 a wasan farko

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai