Majalisa za ta amince da kasafin kudin badi a watan Disamba
Kasafin kudin na 2022 da Buhari ya gabatar ya kai naira tirliyan 16 da digo 39.
Majalisar Dattawa ta bayyana ranakun 15 da 16 ga watan Dasumba na jibi a matsayin lokacin da za ta amince da kasafin kudin kasar nan na badi.
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Majalisar, Sanata Barau Jibrin ne ya bayyana hakan bayan zaman majalisar da aka gudanar a a yau Litinin.
- Iran za ta karbi bakuncin tattaunawa kan makomar Afghanistan
- Tsohon Sakataren wajen Amurka bakar fata na farko ya mutu
Sanata Barau ya ce Majalisar za ta gudanar da sauraron Ministoci da Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomi yayin kare kasafin kudin ma’aikatunsu tun daga ranar 18 ga watan Oktoba har zuwa 5 ga watan Nuwamba.
A cewarsa, sauran kwamitocin da za su yi aiki a kan Kasafin Kudin za su kammala nazari da bincike sannan su gabatar da rahotonsu a ranar 24 ga watan Nuwamba.
Muhimmin aiki a bitar kasafin Kudin shi ne kira da kwamitocin Majalisar ke yi wa shugabanin Hukumomi da ma’aikatun Gwamnati daya bayan daya suna kare kasafin ma’aikatunsu wanda yakan taimaka wa Majalisar wajen tantance wasu batutuwan da aka kiyasta cikin kasafin.
Sanata Barau ya ce za a fara wannan bita da nazari tun daga ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamba har zuwa Talata, 7 ga watan Dasumba.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 7 ga watan Oktoba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2022 a gaban zaman hadin gwiwa na ’yan majalisun tarayyar kasar.
Buhari ya ce kasafin na shekarar 2022, zai mayar da hankali ne wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta soma kuma kudurin kasafin kudin na 2022, wanda ya kai naira tirliyan 16 da digo 39.
Wannan Kudi dai kari ne a kan naira tiriliyan 13.98 na kasafin kudin shekara 2021.
A kan haka ne Gwamnatin Buhari ta bayyana aniyyar ciyo karin bashi don samun karin kudi har Naira tiliyan 6 da biliyan 258, da za ta cike gibin da za a samu a kasafin kudin da shugaban ya gabatar na shekarar 2022.