Majalisa za ta binciki Babban Sufeton ’Yan sanda kan zargin Sanata Misau
Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti na musamman don binciken Babban Sufeton ’Yan sanda, Ibrahim Idris, kan zargen-zargen da Sanata Isah Hamma Misau ya yi masa na cin hanci da rashawa. Kwamitin wanda ya kunshi Mai Tsawatarwa ’Yan Majalisar, Sanata Francis Alimikhena dan jam’iyyar APC daga jihar Edo a matsayin shugaba, an kafa shi ne bayan […]
Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti na musamman don binciken Babban Sufeton ’Yan sanda, Ibrahim Idris, kan zargen-zargen da Sanata Isah Hamma Misau ya yi masa na cin hanci da rashawa.
Kwamitin wanda ya kunshi Mai Tsawatarwa ’Yan Majalisar, Sanata Francis Alimikhena dan jam’iyyar APC daga jihar Edo a matsayin shugaba, an kafa shi ne bayan da Sanata Misau ya ja hankalin ’yan majalisar kan batun a lokacin zaman majalisar.
Majalisar ta mika zarge-zargen da Sanata Misau ya yi ga kwamitin da’a na majalisar wanda Sanata Samuel Anyanwu daga jihar Imo yake shugabanta.