Majalisa za ta binciki matsalar rashin ruwa a Jos
Majalisar Dokokin Jihar Filato ta kafa kwamitin da zai binciki matsalar rashin ruwan sha da ake fama da shi a garin Jos da kewaye.Majalisar ta kafa kwamitin ne bayan da dan majalisa mai wakiltar Mazabar Jos ta Arewa maso Arewa Ibrahim Baba Hassan ya gabatar da kudurinn haka a gaban majalisar.dan majalisar ya ce al’ummar […]
Majalisar Dokokin Jihar Filato ta kafa kwamitin da zai binciki matsalar rashin ruwan sha da ake fama da shi a garin Jos da kewaye.
Majalisar ta kafa kwamitin ne bayan da dan majalisa mai wakiltar Mazabar Jos ta Arewa maso Arewa Ibrahim Baba Hassan ya gabatar da kudurinn haka a gaban majalisar.
dan majalisar ya ce al’ummar Jos da kewaye suna cikin mawuyacin hali sakamakon karancin ruwan sha. “A halin da ake ciki a kullum za ka ga yara da mata suna fita daga gidajensu tun karfe 4:00 na asuba, don neman ruwan da za su yi amfani da shi a gidajensu.”
Ya ce abin takaici ne ganin irin makudan kudin da gwamnatocin baya suka kashe tun daga lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiya don magance matsalar amma babu wani sakamako na kirki da aka gani kan matsalar.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta kawo wa al’ummar Jos dauki kan wannan mawuyacin hali na karancin ruwa da suke ciki.