Majalisa za ta binciki Odua kan hana jirgin katar sauka a Kano

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufurin jiragen sama ya binciki zargin da ake yi wa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama na hana jiragen kasashen waje sauka a filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.An ce Ministar Sufurin Jiragen Sama Misis Stella Oduah ta ki amincewa da bukatar Kamfanin Jiragen Sama na […]

Majalisa za ta binciki Odua kan hana jirgin katar sauka a Kano

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufurin jiragen sama ya binciki zargin da ake yi wa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama na hana jiragen kasashen waje sauka a filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.
An ce Ministar Sufurin Jiragen Sama Misis Stella Oduah ta ki amincewa da bukatar Kamfanin Jiragen Sama na kasar katar na ya rika a Kano.
Da take amincewa da kudirori biyu na bincikar sayen motocin sulke na Naira miliyan 255 da kuma hana jiragen katar sauka a Kano da Mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye Samson Osagie (APC Edo) da Aliyu Sani Madaki (PDP, Kano) suka gabatar, majalisar ta nuna damuwa kan yadda Ministar take gudanar da ayyukanta a ’yan makonnin nan.
Majalisar ta kuma umarci kwamitin ya duba yadda ake gudanar da aikin gyara da zamanantar da filin jirgin na Aminu Kano da niyyar gano ko an keta yarjejeniyar da aka kulla tare da mika rahoto kan haka cikin mako takwas.
Wannan shi ne kamfanin jirgin sama na hudu da aka shi sauka a filin jirgin sama na Malama Aminu Kano.
Kamfanin na katar ya nemi izinin ya rika sauka a Kano da filin jirgin sama na Abuja, kamar yadda Aminiya ta samu bayani.
A farkon bana kamfanonin jiragen sama uku da suka hada da
na – Emirates da naTurkiyya da na Etihad – sun nemi fadada harkokin kasuwancinsu na tashin jiragensu zuwa Abuja da Kano, baya ga Legas inda suke gudanarwa.
Duk da cewa jami’an kamfanin na katar sun ki cewa uffan kan lamarin lokacin da Aminiya ta tuntube su, takardun da ta samu sun nuna kamfanin ya nemi izinin karin wurin sauka daga mahukunta a fannin sufurin jiragen sama don fadada saukar jiragensu zuwa Kano da Abuja fiye da wata hudu da suka gabata, amma ma’aikatar ta ki amincewa da bukatar, maimakon haka ta ba
Kakakin Ministar Joe Obi, ta ki cewa komai kan lamarin lokacin da aka tuntube ta.
Wasu yara a Katsina sun kai Sufeto Janar kotu
Daga Yusha’u A Ibrahim, Katsina da Salihu Makera
Wadansu kananan yara biyu sun gurfanar da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Alhaji Muhammad dahiru Abubakar da wasu mutum hudu a gaban kotu bisa zargin tauye musu hakkinsu na dan Adam.
Masu karar Isiya Ibrahim mai shekara 10 da Bilya Ibrahim mai shekara 15 da suka fito daga karamar Hukumar Dutsin-ma da ke Jihar Katsina, sun nemi Babbar Kotun Jihar Katsina ta daya ta sanya wadanda suke kara su biya su diyyar Naira miliyan 300.
Sauran wadanda suke kara kamar yadda ke kunshe a cikin takardar kara mai lamba KTH/541 M/2013, su ne Hukumar Harkokin ’Yan sanda ta Najeriya da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina da Babban Jami’in ’Yan sanda (DPO) na Shiyyar Dutsin-ma da kuma Shugaban Kwamitin Riko na karamar Hukumar Dutsin-ma.
karar wadda babban lauyansu Barista Anjob Teryange ya shigar a ciki sun bukaci kotun ta bayyana kama su da tsare su da ’yan sanda suka yin a tsawon yini hudu ba tare da bayar da belinsu ba a matsayin a saba wa tsarin mulki da kuma tauye musu ’yancinsu na dan Adam.
Yaran sun yi zargin cewa ’yan sanda sun kama su ‘bisa zalunci’ suka tsare na yini hudu ba tare da beli ba saboda kawai zargin hada baki da aza wutar rikici da taro ba bisa izini ba wadanda a doka ana iya ba da beli a kansu.
Yaran sun kuma nemi kotun ta umarci Sufeo Janar din da sauran wadanda suke kara su nemi gafararsu wadda za a buga a jaridun kasar nan guda hudu da gidajen rediyo ko talabijin biyu.
Sun kuma nemi kotun ta sanya wadanda suke kara su biya su diyyar Naira miliyan 100 kan tsare su ba bisa ka’ida ba da kuma Naira miliyan 200 kan tauye musu ’yancinsu na dan Adam da kuma cin mutuncinsu.