Majalisa za ta halatta ayyukan mazabu-Saraki

  Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce sun amince da kudurin dokar da zai halatta ayyukan mazabu da ’yan majalisar suke gudanarwa don a yi maganin matsalolin da suka dabaibaye lamarin. Da yake jawabi a wurin sauraron ra’ayin jama’a kan kudurorin doka guda uku wanda aka yi masa lakabi da “Ayyukan Mazabu, Kudurin dokar […]

Majalisa za ta halatta ayyukan mazabu-Saraki
Majalisa za ta halatta ayyukan mazabu-Saraki

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce sun amince da kudurin dokar da zai halatta ayyukan mazabu da ’yan majalisar suke gudanarwa don a yi maganin matsalolin da suka dabaibaye lamarin.
Da yake jawabi a wurin sauraron ra’ayin jama’a kan kudurorin doka guda uku wanda aka yi masa lakabi da “Ayyukan Mazabu, Kudurin dokar Tattara kudin shiga na kamfanoni” wanda kwamitin kudi na majalisar dattawan ya shirya, Saraki ya ce kudurin dokar zai tabbatar da cewa an yi la’akari da kowace karamar hukumar  yayin raba kudin kasafin kudi.
“A damokradiyyar kasashen Afirka wadanda suke bin tafarkin tsarin shugaban kasa kamar namu da kasar Kenya da Uganda akwai tsari wanda doka ta tanadar na yadda za a gudanar da ayyukan mazabu”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Hakan shi zai yi maganin duk wata matsala da ka iya tasowa saboda rashin fahimtar lamarin. Ina fatan wannan kuduri zai taimaka wajen gudanar da ayyukan mazabu tare da tabbatar da an yi adalci wajen gudanar da ayyukan”.