Majalisa zata binciki kisan sojojin Najeriya
Majalisar wakilan Najegriya ta kafa kwamitin da zai binciki kisan da aka yi wa sojojin Najeriya sama da 118 a rundunar sojojin bataliya ta 157 da mayakan Boko Haram suka kai masu hari a garin Metele da ke jihar Bormo. Kwamitin zai yi bincike akan karkatar da kudaden da aka ware wajen yakar mahara, kamar […]
Majalisar Wakilai
Majalisar wakilan Najegriya ta kafa kwamitin da zai binciki kisan da aka yi wa sojojin Najeriya sama da 118 a rundunar sojojin bataliya ta 157 da mayakan Boko Haram suka kai masu hari a garin Metele da ke jihar Bormo.
Kwamitin zai yi bincike akan karkatar da kudaden da aka ware wajen yakar mahara, kamar yadda ‘yan majalisar suka bukaci rundunar sojojin da ta fitar sunayen wadanda aka kashe da wadanda suka bace.
Dan majalisa Chukwuka Onyema daga jihar Anambra ne ya gabatar wa zauren majalisar bukatar hakan.