Majalisar Birtaniya ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu

A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan majalisar Birtaniya suka kada kuri’ar amincewa da kafa kasar Falasdinu a matsayin kasa mai ‘yanci, a wani mataki da ke karfafa gwiwar al’ummar Falasdinu a fafutukarsu ta neman kasar kansu. Kodayake, Birtaniya ba ta bayyana Falasdinu a matsayin kasa ba tukuna, amma ta ce za ta iya […]

Majalisar Birtaniya ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu
Majalisar Birtaniya ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu

A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan majalisar Birtaniya suka kada kuri’ar amincewa da kafa kasar Falasdinu a matsayin kasa mai ‘yanci, a wani mataki da ke karfafa gwiwar al’ummar Falasdinu a fafutukarsu ta neman kasar kansu.

Kodayake, Birtaniya ba ta bayyana Falasdinu a matsayin kasa ba tukuna, amma ta ce za ta iya yin hakan a kowane lokaci a fatanta na samar da zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Yahudawa. Firaministan Birtaniya Dabid Cameron ya kaurace wa zaman majalisar, wanda jagoran ’yan adawa ya kira. Kuma mai magana da yawun Mista Cameron ya bayyana cewa sakamakon kuri’ar ba zai shafi harkokin kasashen wajen kasar ba.
Har ila yau, hukumomin Falasdinawa da na Isra’ila sun kalli zaman majalisar ta akwatin talabijin, musamman ma saboda kowannensu yake neman goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai da kuma majalisar dinkin duniya.
kudirin da ya samu nasara da kuri’u 274 bisa 12 na kin amincewa, ya bukaci gwamnatin Birtaniya da ta amince da kasar Falasdinu a bangare guda, a daya bangaren kuma kasar Isra’ila.
Har ila yau, kuri’ar na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin kasar Sweden take shirin amince wa da Falasdinu a matsayin kasa. Wani mataki da kasar Isra’ila ta yi Allah-wadai, inda take bai wa Falasdinawa ’yanci zai iya samuwa ne kawai ta hanyar tattaunawa.