Majalisar Borno za ta jingine zamanta saboda Ndume

Majalisar Dokokin jihar Borno ta yi barazanar jingine zamanta har na tsawon kwanaki 30, matukar Sufeto Janar na ‘Yan sanda bai bincika tare da daukar mataki dangane da marin da Sanata Muhammad Ali Ndume ya yi wa dan Majalisar Dokokin Jihar Borno, mai wakiltar Damboa, Hon. Habu Daja, a gidansa a karshen makon jiya ba. […]

Majalisar Borno za ta jingine zamanta saboda Ndume

Majalisar Dokokin jihar Borno ta yi barazanar jingine zamanta har na tsawon kwanaki 30, matukar Sufeto Janar na ‘Yan sanda bai bincika tare da daukar mataki dangane da marin da Sanata Muhammad Ali Ndume ya yi wa dan Majalisar Dokokin Jihar Borno, mai wakiltar Damboa, Hon. Habu Daja, a gidansa a karshen makon jiya ba.

Wannan marin da Sanata Mai Wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya yi ga dan majlisar dokkokin jihar, ya janyo cece-ku ce a siyasar Jihar Borno, inda wasu ke ganin cewa wannan mari bai ma faru ba, a yayin da wasu ke cewa an yi wannan mari domin a kan idonsu aka yi. Malam Muhahammad Bello, yana daya daga cikin wadanda abin ya faru a gabansu wanda kuma yake bangaren Sanatan, sannan kusa ne a APC na Damboa.

“Wannan mari da ake cewa Sanata Ali Ndume ya yi wa Hon Abu Daja babu kamshin gaskiya ko kadan bai faru ba, domin a ranar 22 ga Oktoba muka dunguma muka je gidan shi Sanatan da nufin ya sasanta wata rigima, to bayan an kammala taron sai ya dauko kudi ya bai wa matasanmu, to akwai daya daga cikinsu da ya nuna kudin sun yi masu kadan sannan sai ya rika fadin wasu maganganu wadanda ba su dace ba, sai Sanatan ya juya wajen dan Majalisar Dokokin ya nuna masa yatsa tare da cewa kai Habu Daja kai ne ka kawo wadannan matasan har gidana don su ci mini mutunci ko? To abin da ya faru ke nan, ya nuna masa yatsa amma bai mare shi ba, domin zan iya rantsewa da Alkur’ani cewa bai mare shi ba.” 

“Sannan su kuma ‘Yan Majalisa bai kamata a ce su tsayar da ayyukansu kawai saboda wasu daban ba, to shike nan sun tsayar da Ayyukansu, to talakawa kuma fa? Mu shiga cikin wahala ke nan? Ai ina ce a Majalisa akwai kwamitoci da akan nada don su binciki irin wadannan abubuwan idan an kama mutum da laifi shike nan sai a gurfanar da shi a gaban hukuma idan kuma bai kama mutum da laifi ba, ka ga kenan salin alin babu abin da zai shafi talakawa, a saboda haka ina kira ga ‘Yan Majalisar dokokin jiha da su janye wancan magana ta dakatar da zamansu su dawo su kafa kwamitin bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin, amma ba wai su kai kara wajen Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ba har abin ya shafi talakawa, amma gaskiyar zance wannan mari ba a yi ta ba, ni zan iya bayar da shaida a gaban ‘Yan Majalisar dokokin da kuma a gaban Sufeto Janar na ‘Yan Sandan ko da ko ta kama in rantse da Alkur’ani ne.’’ in ji Muhahammad Bello. 

Shi ko Alhaji Gaji Damboa, Jami’in watsa labarai da hulda da Jama’a na Jam’iyyar APC a karamar Hukumar Damboa, wanda yake bangaren dan Majalisar Dokokin jihar Habu Daja, wanda shi ma aka yi abin a gabansa, ya tabbatarwa da wakilinmu cewar “Ko shakka babu Sanata Ali Ndume ya mari wannan dan majalisa namu, domin a gabana abin ya gudana bayan da muka shiga gidan Sanata Ali Ndume tare da Hon. Daja, mun kammala taronmu ke nan sai shi Ndume ya ba mu kudi har Naira dubu 200, shi ne sai wani matashi ya bude baki ya ce wannan kudi  ya yi mana kadan domin muna da yawa, sannan kuma yau shekaranmu biyu ke nan ba ma haduwa da kai balle ka ba mu wani abu, to wannan lokacin da muka samu dama ya kamata a ce abin ya fi haka, shike nan sai Sanata ya tashi yana ta fadace-fadace har yana cewa shin kai ne za ka fada min abin da zan ba ku?” 

“Sai ya juya wajen Hon. Abu Daja, ya ce kai ne ka kawo mini wadannan yaran da suke ci mini mutunci har gidana ko? Shike nan sai ya mare shi! A gabana aka yi wannan kuma ko da Alkur’ani zan rantse wannan mari an yi shi, saboda haka ina goyon bayan matakin da Majalisar Dokoki ta Jihar Borno ta dauka na dakatar da ayyukansu na wata guda don jawo hankalin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda don duba lamarin, tun da yake dai shi ya ce bai mare shi ba, kuma ni a kan idona ya mare shi,’’ in ji Dambua.

 A yanzu haka dai Majalisar Dokokin jihar ta jingine ayyukanta kamar yadda ta yanke hukunci a zamanta na baya, tana sauraron Sufeto Janar na ‘Yan Sanda don kaddamar da bincike tare da daukar mataki kan Sanata Ali Ndume.