Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Natasha na wata 6

Majalisar za ta tattauna game da shawarar dakatar da Sanata Natasha tare da zartar da hukunci.

Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Natasha na wata 6

Kwamitin Majalisar Dattawa ya bayar da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida.

Kwamitin ladabtarwa da ɗa’a ne, ya bayar da shawarar biyo bayan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, kan cin zarafinta.

A zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis, Shugaban kwamitin, Neda Imasuen, ya gabatar da rahoton kwamitin, inda ya bayyana cewa Natasha ta ƙi bayar da haɗin kai wajen binciken da aka yi.

Kwamitin ya kuma bayar da shawarar a dakatar da biyanta albashi tare da janye mata jami’an tsaron da ke kula da ita.

Rikicin ya fara ne bayan da Sanata Natasha ta zargi Akpabio da ƙin amincewa da wasu ƙudurorinta, musamman wanda ya shafi Kamfanin Ƙarafa na Ajaokuta.

Haka kuma, ta ce Akpabio ya kira ta da suna “yar kulob” a zaman Majalisar, kodayake daga baya ya ba ta haƙuri.

A martaninsa, Akpabio ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya bayyana cewa yana girmama mata kuma bai aikata wani abin da bai dace ba.

Wasu Sanatoci sun samu bambancin ra’ayi game da hukuncin dakatarwar.

Sanata Abba Moro daga Benuwe ta Kudu, ya bayar da shawarar a rage wa’adin dakatarwar zuwa watanni uku kawai, yayin da wasu ke goyon bayan hukuncin watanni shida.

Yanzu Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rahoton kwamitin domin yanke hukunci na ƙarshe.