Majalisar Dattawa ta amince a ninka albashin ma’aikatan shari’a sau uku

Ƙudirin dokar ya tsallake karatu na uku a zaman majalisar na ranar Laraba.

Majalisar Dattawa ta amince a ninka albashin ma’aikatan shari’a sau uku

Majalisar Dattawa ta amince da wani ƙudirin da ke neman ninka albashin Alƙalin Alƙalai Olukayode Ariwoola da sauran manyan alƙalan ƙasar sau uku.

Ƙudirin dokar ya tsallake karatu na uku a zaman majalisar na ranar Laraba.

Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin shari’a da ’yancin ɗan Adam da kuma harkokin shari’a na majalisar, wanda shugabansa Mohammed Monguno ya gabatar.

Ɗan majalisar ya ce “biyan wadataccen albashi ga ma’aikatan shari’a zai ba su damar mayar da hankali wajen gudanar da aikinsu ba tare da tunanin wani nauyi na daban ba.”

A cewarsa: “Ƙarin albashin zai inganta ƙwarewar aikin ma’aikatan shari’a, lamarin da kuma zai dawo da martabar ɓangaren shari’a a tsakanin jama’ar ƙasa.”

Ya kuma bayyana cewa an shigar da tanadin wannan ƙari na albashin ma’aikatan shari’a a cikin ƙaramin Kasafin Kuɗin 2024.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan mataki na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa majalisar ƙudurin na neman sahalewarta kan yi wa ma’aikatan shari’ar ƙarin albashi.

Brighton ta doke Manchester City a Firimiyar Ingila

Babu wata addu’a da na shirya kan matsin rayuwa — Remi Tinubu

Tinubu zai halarci taron ƙasashen Larabawa da Musulunci a Saudiyya

Obaseki ya rushe dukkanin muƙarraban gwamnatinsa