Majalisar Dattawa ta amince da kara wa’adin dokar ta-baci

’Yan Majalisar Dattawa sun amince da kara wa’adin dokar ta-baci da wata shida a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da maharani da ake jinginawa ga Boko Haram suke tayar da kayar baya.Sanatoci sun amince ci gaba da aiki da dokar a jihohin ne a kuri’ar da suka kada, a ranar Talatar da ta gabata, […]

Majalisar Dattawa ta amince da kara wa’adin dokar ta-baci
Majalisar Dattawa ta amince da kara wa’adin dokar ta-baci

n Sanata David Mark, Shugaban Majalisar Dattawa’Yan Majalisar Dattawa sun amince da kara wa’adin dokar ta-baci da wata shida a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da maharani da ake jinginawa ga Boko Haram suke tayar da kayar baya.
Sanatoci sun amince ci gaba da aiki da dokar a jihohin ne a kuri’ar da suka kada, a ranar Talatar da ta gabata, tuni takwarorinsu na Majalisar Wakilai suka amince da karin wa’adin duk da adawar da sanatocin da suka fito daga jihohin da dokar ke aiki da dattawan jihohin suka nuna.
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ne ya bukaci a kara wa’adin dokar bayan abin da ya kira ci gaba da tashin hankali a jihohin babban kalubale ne, inda ya nuna damuwa kan zubar da jinin fararen hula da ake ci gaba da yi.
A ranar 14 ga Mayun bara ne Gwamnatin Tarayya ta kafa dokar ta-baci a jihohin uku da niyyar murkushe kungiyar Boko Haram, wadanda suka tayar da kayar baya tun shekarar 2009.
An tura daruruwan sojoji zuwa jihohin kuma aka sanya dokar hana fitar dare wani lokacin ma har da rana, tare da tsaurara matakan tsaro ciki har da yanke layin waya don hana tsara kai hare-hare a tsakanin ’ya’yan kungiyar.
Sai dai duk da daukar wadannan matakai, ’ya’yan kungiyar ta Boko Haram sun ci gaba da kai hare-hare, inda a watan Nuwamban bara Shugaba Jonathan ya nemi a kara wa’adin dokar da wata shida.
Sai dai a farkon wannan shekarar kadai kungiyar ta yi sanadiyyar halaka kimanin mutum dubu biyu, wanda ake ganin hakan ne ya sanya Shugaba Jonathan kara bukatar a dada wa’adin dokar.
A lokacin da sanatocin ke amincewa da bukatar sun kuma yi maraba da goyon bayan da kasashen duniya suke bayarwa a kokarin da ake yin a kwato ’yan matan Chibok sama da 200 da Boko ta sace tun ranar 14 ga Afrilun da ya gabata.
Sanatocin sun kuma bukaci sojoji su yi amfani da karfinsu wajen murkushe ayyukan Boko Haram.
Majalisar dai ta amince da bukatar ce bayan wata tattaunawar sirri da ta gudanar saboda rarrubuwar kawunan da aka samu tsakanin sanatoci kan batun.
Sanatocin sun samu rarrabuwar kawuna ne bisa dalilai na bambancin jam’iyyun siyasa da kuma bangaranci.