Majalisa ta dakatar da Wike daga yin rusau a Abuja
Majalisar ta kafa kwamiti mai mambobi takwas domin bincikar yadda Wike ya rushe wa mutane kadarori.
Majalisar Dattawa ta buƙaci Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya dakatar da rushe gine-ginen da yake yi, sai da izinin kotu.
Haka kuma, ta kafa kwamiti mai mambobi takwas ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, domin bincikar rusau ɗin da aka fara tun daga lokacin da Wike ya zama ministan Abuja.
- Ina nan a raye, ban mutu ba – Shugaban INEC
- Zamana a gidan yari jarabawa ce daga Allah – Farouk Lawan
Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da Sanata Ireti Kingibe ta gabatar a zaman majalisar.
A cewar Kingibe, rushe gine-gine da ministan ke yi ya saɓa hukuncin kotu, kuma yana ƙara ta’azzara rayuwa a birnin.
Ta ce rusau ɗin ya sa mutane da dama sun faɗa cikin mawuyacin hali, don haka ta buƙaci majalisar ta tilasta wa Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta dakatar da ƙwace kadarorin jama’a.