Majalisar dattawa ta dage ranakun tantance Ministoci
Majalisar dattawan Najeriya ta dage ranakun tantance sunayen sabbin Ministocin da Shugaba Buhari ya aikawa zauren majalisar a yau, wanda tantancewar za ta kai makon gobe. A yau Talata ne shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya karanta sunayen sabbin Ministoci 43 da shugaba Buhari ya amince nada su a mukaman Ministocin Najeriya. Shugaban Kwamitin wucin […]
Majalisar dattawan Najeriya ta dage ranakun tantance sunayen sabbin Ministocin da Shugaba Buhari ya aikawa zauren majalisar a yau, wanda tantancewar za ta kai makon gobe.
A yau Talata ne shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya karanta sunayen sabbin Ministoci 43 da shugaba Buhari ya amince nada su a mukaman Ministocin Najeriya.
Shugaban Kwamitin wucin gadi na fannin watsa labarai da hulda da jama’a na majalisar Dattawan Sanata Adeyeye Adedayo, ne ya sanar da hakan ga manema labarai.
Sanata Adeyeye, ya kara da cewa Kwamitin zai yi zama na musamman akan matakan tantance sabbin Ministocin da za a fara daga gobe.