Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6

Bayan tattaunawa da gabatar da rahoton kwamitin, Majalisar ta amince ta dakatar da Natasha na watanni shida.

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida.

Wannan hukunci ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar, wanda ya bincike ta kan zargin karya dokokin majalisar.

Sanata Natasha ta ƙi bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba, duk da gayyatar da aka yi mata domin ta kare kanta.

A sakamakon haka, majalisar ta yanke hukuncin dakatar da ita har na tsawon watanni shida.

’Yar majalisar ta shiga takun saƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan rabon kujeru a zauren majalisar.

Haka kuma, Natasha ta zargi Akpabio da cin mutuncinta a bainar jama’a da kuma hana ta gabatar da ƙudirorinta a zauren majalisar.

Ƙin amincewarta da sabon tsarin rabon kujeru ya sa Shugaban Majalisar ya hana ta damar yin magana a zauren, wanda hakan ya haifar da saɓani a tsakaninsu.

A sakamakon haka, majalisar ta tura batun zuwa Kwamitinta na Ladabtarwa da Ɗa’a don gudanar da bincike.

A zaman kwamitin na ranar Laraba, Shugaban Kwamitin, Sanata Neda Imasuen (PDP, Edo ta Kudu), ya nuna takaicinsa kan rashin halartar Natasha.

Ya ce: “Sanata Natasha an gayyace ta zuwa wannan taro. Muna fatan za ta zo yayin da muke ci gaba da zama.”

Rashin halartar ya sanya majalisar yanke hukuncin dakatar da ita na tsawon watanni shida masu zuwa.