Majalisar Dattawa ta umarci Hafsan Hafsoshin Soja ya mayar da ofishinsa Maiduguri
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa ya umarci Hafsan Hafsohin Sojan Najeriya Laftana Janar Kenneth Minimah ya mayar da ofishinsa Maiduguri na wucin gadi. Kwamitin a karkashin Sanata Thompson Sekibo ya bukaci haka ne a daidai lokaci da yake tantance kasafin kudin tsaro na bana.Sanata Sekibo ya ce kwamitin ya yi tir da ayyukan Boko Haram, […]
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa ya umarci Hafsan Hafsohin Sojan Najeriya Laftana Janar Kenneth Minimah ya mayar da ofishinsa Maiduguri na wucin gadi. Kwamitin a karkashin Sanata Thompson Sekibo ya bukaci haka ne a daidai lokaci da yake tantance kasafin kudin tsaro na bana.
Sanata Sekibo ya ce kwamitin ya yi tir da ayyukan Boko Haram, kan yadda suke cutar da fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, a yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce wannan yana daga cikin matakan da aka dauka don shawo kan matsalar Boko Haram, sannan kwamitin ya bukaci a samar da matakan tsaro ga makarantu da cibiyoyin kula da lafiya, tun daga yanzu har zuwa wani lokaci.
“Mun ji kana yunkurin komawa Maiduguri, don haka a kwmaitinmu za mu rika lura da ayyukan da za ka rika gudanarwa, muna kuma bukatar ofishinka ya koma Rundunar Soja ta Bakwai da ke Maiduguri. Mun kuma dauki matakin ne don ganin ka yi aiki tukuru wajen shawo kan mummunan halin da ake kaiwa. Sannan akwai bukatar shugaban sojojin ya bullo da wasu dabaru don shawo kan wuce gona da irin da sojoji ke yi, tare da samar da isassun kayan aiki don tunkarar masu kunar bakin wake,” inji Sanata Sekibo.
Ya ce, bisa la’akari da halin da ake ciki, kwamitin zai karbi tsare-tsaren kasafin kudin ba tare da ya yi bitarsa dalla-dalla ba.
“Babu wanda zai taka rawa a dandali alhali gidansa yana cin wuta. Abin da ya fi damunmu, shi ne magance kunar bakin wake, ta yadda ’yan Najeriya za su samu kariya da kwarin gwiwa,” inji shi.
Kwamitin ya kuma bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya samar da isassun kayan aiki ga rundunar sojojin don tunkarar kalubalen da ke gabanta. “Dole a samu galabar wannan yaki matukar kasarmu za ta ci gaba da dorewa a matsayin dunkulalliyar kasa tare da hadin kan al’umma,” a cewar Sanata Sekibo.
Kuma ya ce, kwamitin zai kai ziyara a jihohi uku da wannan bala’i ya shafa da zarar majalisa ta dawo daga hutunta.
Da yake mayar da jawabi, Janar Kenneth Minimah, ya ce rundunar sojan na bukatar karin kudi. Ya kuma ba kwamitin kwarin gwiwar cewa sojoji za su iya tunkarar wannan kalubale, dan lokaci kawai za a dauka kafin a karya lagon masu hare-haren kunar bakin waken.
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Sanata bictor Ndoma-Egba, ya bayyana kisan gillar da aka yi wa dalibai a ranar Litinin da ta gabata a Jihar Yobe a matsayin “wuce gona da iri.”